<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>In Na Yi Tunani Sosai LW423</title>
<lyrics>[V1]
 1) In na yi tunani sosai
 Kan zuwan Ubangijina
 Da yadda ni zan tsaya dai
 Ko murna ko kuwa hawaye.

[V2]
 KORUS
 Yesuna, Yesuna,
 Ka tsarkake ni tun yanzu,
 Kada ka rage kome nan
 Ya zama kaya na Shaiɗan
 Yesuna, Yesuna
 Ka tsarkake ni tun yanzu.

[V3]
 2) Kada a ranar zuwansa
 Ya iske ni da zunubi
 Lalle in ɓoye fuska ta,
 In ce, &quot;Ya Allah, me zan yi?&quot;
 Korus

[V4]
 3) Ran da ka kira ni in zo,
 Domin ka gwada aikina,
 Idan wuta ta cinye duk
 Ina misalin kukata ?
 Korus

[V5]
 4) Ya Yesu, ji addu'ata
 Ka ba ni  ƙargin zuciya
 In kama aikinka sosai
 In tarbe ka da daɗin rai.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>423</hymn_number>
</song>